On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Manchester United Ta Lallasa Liverpool Da Ci 4 Babu Ko Daya

MANCHESTER UNITED DA LIVERPOOL

Erik Ten Hag ya ce ya gamsu da yadda ya fara takunsa da kafar dama a matsayin mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.

Sai dai kuma ya baiyana cewa ba zai bari nasarar  da  ya samu ta  dauke masa hankali ba,  bayan doke abokan hamayyar su Liverpool da ci 4 da nema  a wasan sada zumunta na share fage  da suka yi a  Thailand.

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester  United ta fara  wasan da karfi  inda  ta samu nasarar jefa kwallaye ukku a ragar  kungiyar kwallon kafa ta  Liverpool tun kafin a tafi hutun rabin lokaci, inda  ya wasa  Jadon Sancho da Fred da Anthony Martial  suka samu nasarar zura kwallaye a  filin wasa na Rajmangala dake Bangkok, duk da kasancewar  babu  dan wasa  Cristiano Ronaldo, wanda yayi balaguro saboda wasu abubuwa da suka danganci iyali.

Dukannin masu  horar da kungiyoyin sun sauye-sauye da yawa a cikin mintuna 90, a yayin da mai horaswa  Jurgen Klopp na Liverpool  ya mamaye wasa a zagaye na biyu  kafin dan wasa  Facundo Pellistri ya ciwa  united kwallo ta  hudu.