On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Manyan Lauyoyi Masu Lambar SAN Zasu Kare Kungiyar ASUU A 'Karar Da Gwamnatin Taraiyya Ta Kaita

LAUYOYI MASU LAMBAR KWAREWA TA SAN

Manyan Lauyoyi masu lambar kwarewa ta SAN dake karkashin kungiyar Malaman Jami’oi ta kasa ASUU ne zasu kare kungiyar, a shari’ar da za’a fara tsakanin kungiyar da gwamnatin taraiyya a yau a kotun Ma’aikata ta kasa.

Gwamnatin taraiyya ta maka kungiyar kotu a sakamakon kin janye dogon yajin aikin data soma tun a ranar  14 ga watan Fabarairun bana.

Bayan kokarin kawo karshen yajin aikin yaci tura, gwamnatin taraiyya ta dauki matakin garzayawa gaban kotun ma’aikata ta kasa domin kalubalantar matakin tafiya yajin aikin.

A zantawarsa da jaridar PUNCH, Wani dan kungiyar ASUU wanda bai bukaci a baiyana sunansa ba, Yace  kungiyar zata yi amfani da ‘ya’yan wadanda suka kasance manyan lauyoyi ne domin kare kudirinta a gaban kotun.

 

More from Labarai