On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Masana Sun Kare Matakin Matatar Man Dangote na Sayar da Man Fetur da Dala

Wasu masana harkokin masana'antu sun kare matakin da Matatar Dangote ta dauka na karbar dalar Amurka wajen sayar da kayayyakin albarkatun man fetur din ta.

Masanan bayyana cewa matakin ya dace da yanayin kasuwar makamashi da tattalin arziki a halin yanzu.

Masanan sun bayyana cewa bai kamata a dauki wannan mataki a matsayin wani abu da zai cutar da jama'a kai tsaye ba, domin a cewarsu, kamfanoni masu zaman kansu suna da hakkin tsara yadda za su gudanar da kasuwancinsu domin kare dorewarsa da kuma rage illolin sauyin farashin kudaden kasashen waje.

Sai dai matakin ya haifar da muhawara a tsakanin masu ruwa da tsaki a bangaren man fetur, inda ake nuna damuwa cewa zai iya haifar da karin farashin fetur, kara hauhawar farashin kayayyaki da kuma janyo karin matsin lamba kan kasuwar musayar kudaden kasashen waje.

Da yake magana akan batun, masanin tattalin arziki, Wilson Agaba, ya ce sabon tsarin zai tilasta wa dillalan man fetur neman dalar Amurka ko kuma su biya kwatankwacinta a naira domin samun fetur daga matatar.

A cewarsa, hakan na iya kara yawan bukatar dalar Amurka a kasuwa, abin da zai iya kara matsin lamba kan darajar naira idan ba a dauki matakan da suka dace wajen daidaita kasuwar musayar kudade ba.

Ya kara da cewa yadda sabon tsarin zai shafi farashin man fetur a kasuwa zai dogara ne da yadda dillalai za su dauki karin kudin da za su kashe wajen sayen fetur, da kuma yadda gwamnati da hukumomin da abin ya shafa za su tafiyar da manufofinsu na tattalin arziki a nan gaba.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 35°C | Low: 23°C