On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Masana'antun Saka Sun Durkushe Saboda Rashin Yin Amfani Da Tufafin Da Ake Samarwa A Najeriya.

Masana'antun Sa'ka

Hadaddiyar Kungiyar Masu Masana’antun Saka da Jima da kuma Dinki ta kasa, Ta Alakanta Matsalar durkushewar Masana’antun Saka da aka samu a kasar nan, Da rashin yin amfani da Tufafin da kanfanonin saka na cikin gida da gwamnatin Taraiyya da kuma Hukumominta ke samarwa.

Shugaban kungiyar na kasa, John Adaji ne ya baiyana haka lokacin da yake amsa tambaya game da tasirin da aka samu  game da bilyoyin kudaden da gwamnatin taraiyya  ta saka a bangaren  Masana’antun Saka  domin farfado dasu a shekarar  1986 da kuma shekarar 2020……insert.

A cewar Kwamared Adaji, Makudan kudin da ake kashewa wajen aikin sa’ka da kuma karancin wutar lantarki, da kuma karuwar shigo da jabun kayayyaki sun taka rawa wajen durkushewar Masana’antu  a kasar nan.

A zantawarsa da wakilinmu Victor Chiristopher, Kwamared Adaji ya baiyana damuwarsa game da gazawar gwamnati  na kin hana shigo da kayayyakin da suka danganci Tufafi zuwa cikin kasar nan