On Air Now

ZANGON MARAICEN LAHADI

6:00pm - Midnight

Masar Ta Budewa 'Yan Najeriya Iyakokinta

Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare, Ta baiyana cewar jirgin rundunar sojan sama ta kasa ya shirya tsaf domin dauko ‘yan Najeriyar da suka makale zuwa gida Najeriya, To sai dai har zuwa wannan lokacin iyakokin kasar Masar suna a kulle.

Bugu  ta  baiyana cewar  tawagar  jami’an rundunar sojin sama  ta kasa sun tashi zuwa  filin jirgin saman Aswan tun ranar Asabar din data gabata, domin kwaso mutanen, tare da fatan  za’a  samu  matsaya.

To sai dai kuma daga bisani shugabar  Hukumar kula da ‘yan Najeriya  mazauna kasashen ketare, Uwargida  Abike dabiri  Erewa    ta  tabbatar da cewar  Hukumomin kasar  sun bude  kan iyakokin nasu, domin baiwa  ‘yan Najeriya damar  shiga kasar,bayan da shugaban kasa  muhammadu Buhari  ya  tsoma  bakinsa cikin takkadamar.