Hukumar Kwallon Kafar Masar ta bukaci FIFA ta gudanar da bincike kan alkalan da suka jagoranci wasan da Argentina ta doke Masar da ci 3-2 a zagayen 'yan 16 na gasar cin Kofin Duniya.
Hukumar ta ce shugabanta, Hany Aburida, ya shigar da ƙorafi ga FIFA, yana zargin alkalan da aikata manyan kura-kurai da kuma nuna bambanci, wanda ya ce ya jawo Masar ta fice daga gasar.
Ƙorafin ya haɗa da soke ƙwallon da Mostafa Ziko ya ci bayan VAR ta gano cewa an yi wa Lisandro Martinez laifi tun farkon harin, yayin da Masar ke kan gaba da ci 1-0, sannan kuma ƙin bai wa Masar bugun fenariti bayan Alexis Mac Allister ya ja Hamdy Fathy kafin Enzo Fernandez ya ci ƙwallon nasarar Argentina.
Hukumar ta kuma bukaci FIFA ta cire alkalin wasa François Letexier da dukkan tawagar alkalansa daga ci gaba da gudanar da wasannin gasar idan bincike ya tabbatar da kura-kuran da kuma zargin nuna wariya ga tawagar Masar.
Comments
Add a comment