Mai Bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu Shawara Kan Harkokin Sadarwa da Manufofi, Daniel Bwala, ya ce 'yan Najeriya da dama da suka koma ƙasar Birtaniya domin neman ingantacciyar rayuwa na fuskantar ƙalubale masu yawa, inda wasu ke yin ayyukan da ba su dace da iliminsu ba.
Da yake magana a shirin The Morayo Show, Bwala ya ce mutane da dama masu digirin farko da na biyu daga Najeriya suna aiki ne a cibiyoyin kula da marasa lafiya da tsofaffi, duk da irin manyan takardun karatun da suke da su.
Ya bayyana hakan a matsayin wani nau'in "bautar zamani."
Bwala, wanda ya ce shi ma mazaunin Birtaniya ne, ya gargadi 'yan Najeriya da kada su ɗauka cewa duk wanda ya ƙaura zuwa ƙasashen waje yana rayuwa cikin jin daɗi.
Ya ce duk da ingantattun ababen more rayuwa da ake samu a can, tsadar rayuwa na hana mutane da dama cimma burinsu na mallakar gida ko mota.
Ya ƙara da cewa ko da yake rashin aikin yi na ci gaba da zama ƙalubale a Najeriya, masu ƙaramin albashi a gida na samun tallafin iyali, damar karɓar bashi da kuma sauƙin kashe kuɗin rayuwa fiye da yadda ake samu a Birtaniya.
Ya kuma ce hakan ne ya sa 'yan Najeriya da ke Amurka ke yawan aikowa da kuɗi gida fiye da waɗanda ke zaune a Birtaniya.
Comments
Add a comment