On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Masu Furta Kalaman Kiyayya Ka Iya Fuskantar Daurin Shekara 10 Da Tararar Milliyan 40 A Najeriya

Wani kudurin doka da ke neman kafa hukumar da ke yaki da laifukan zabe a Najeriya, wanda majalisar dokoki ke nazari a kai, ya gabatar da kudirin sanya kalaman nuna kiyayya ko batanci a matsayin laifin zabe da zai iya janyo zaman gidan yari na shekara 10 ko  tarar Naira milliyan 40 ko kuma duk biyun.

Kwamitin Majalisar Wakilai mai kula da al’amuran zabe ya gudanar da taron jin ra’ayin jama’a kan kudirin 2022 na dokar kafa hukumar laifukan zabe ta kasa da kuma abubuwan da suke da alaka da hakan da akayi jiya a Abuja.

A wurin taron hukumar zabe mai zaman kanta da kwamitin hadakar jam’iyyun siyasa da dai sauransu sun goyi bayan kudirin amma hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta ki amincewa da shi.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, a nasa jawabin, ya bukaci majalisar dokokin kasarnan da ta dauki mataki na gaba ta hanyar samar da kotu ta musamman kan laifukan zabe.