On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Masu Garkuwa Sun Sace Shugaban Wata Karamar Hukuma A Jihar Taraba

MASU GARKUWA

Masu garkuwa da mutane sun sace shugaban karamar hukumar Takum dake jihar Taraba, mai suna Boyi Manja, inda suka halaka dogarinsa a yayin harin da suka kai.

An sace  shugaban karamar hukumar ne  a  garin Kofai Ahmadu  dake  kusa da kan hanyar  Takum zuwa Wukari  a  ranar Lahadi.

Wani abokinsa wanda  ya nemi a sakaye  sunansa,  Ya  ce an  harbe  dogarin shugaban karamar  hukumar ne a lokacin da suke musayar  wuta  tsakaninsa da  masu garkuwar,Kafin su dauke  shi.

Majiyar  ta baiyana cewar  shugaban karamar hukumar tare da mai tsaron lafiyar tasa da  kuma Direbansa  sun bar  birnin Jalingo zuwa  Takum ne,  Inda  masu garkuwar  suka rika  bin sawunsu.

Kakakin rundunar  ‘yansandan jihar , Abdullahi  Usman  ya  tabbatar da   faruwar  lamarin.