On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Masu Sana'ar POS Sun Koma Sayen Sabbin Kudi A Gidajen Mai

POS

Babu shakka abunda mutum ke tsammanin ana siyarwa a gidajen Mai shine man fetir , To sai dai a halin yanzu ta sauya zani, a yayin da wasu gidajen man a jihar Naija suka zama wuri hada-hada ta canjin kudi.

Hakan ya biyo bayan yadda  a yanzu masu sana’ar POS  abirnin Minnan jihar Naija suke  siyan sabbin takardun kudi  daga wajen masu gidajen man domin yin harkokin kasuwancinsu na yau da kullum.

Wani mai sana’ar  POS, mai suna Mohammed  Isah  ya  fadawa manema Labarai cewa  ya  samu naira dubu 150  a ranar  Asabar din data gabata, sannan kuma sake  samun wata karin naira dubu 150 din a jiya, daga   gidajen mai daban daban, domin ganin ya biyana bukatar  abokan huldarsa.

Ya  ce  abunda mutum yake  bukata  shine  kulla alaka  da masu gidajen man  domin samun kudin.