On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Masu Satar Mutane Da Safarar Makamai Sun Shiga Hannun ‘Yan Sanda A Jihar Gombe

Jami’an rundunar 'yan sanda a jihar Gombe sunyi nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargi da satar mutane da kuma mallakar makamai be bisa ka’ida ba.

Cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar ASP, Mahid Mu'azu, ya raba wa manema labarai, ya ce mutanen dukkansu daga karamar hukumar Dukku, an kama su ne a kan hanyarsu ta zuwa maboyar da suke taruwa a dajin Yankari da ke Bauchi.

Ya ce, an kama su ne a ranar 19 ga watan Augusta a kauyen Tudun Kwaya da ke karamar hukumar Biiliri tare da hadin gwiwar jami'an sintiri da mafarauta a yankin.

Ya ce koda aka tambayesu sun bayyana cewa suna daga cikin masu satar mutanen da ke addabar mutane a Pindiga.