On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Mataimakan Shugabannin Kananan Hukumomi Na Yiwa Doguwa Zawarcin Gurbin Kujerar Minista Daga Jihar Kano

Kungiyar mataimakan shugabannin kananan hukumomi daga shiyyar Kano ta Arewa, ta yi ga shugaban kasa Bola  Ahamed  Bola Tinubu da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da  dukkannin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC, da su mika  gurbin kujerar Minista daga jihar Kano ga dan majalissa mai wakiltar tudun wada da Doguwa Rt Hon Alhassan Ado Doguwa.

Mataimakin shugaban kungiyar Aminu Bello Gogori, ya yi kiran ne ta cikin wata sanarwar sakon murya da ya fitar.

Gogori wanda kuma shine mataimakin shugaban karamar hukumar Bagwai ta jihar Kano, ya kuma mika kiran ga jagororin APC na kasa da jihar Kano.

Kungiyar ta ce Hon Alhassan Ado Doguwa yana da kwarewa ta aiki da gogayya ta siyasa da zai dace da matsayin na minista.

Haka kuma mataimakin shugaban karamar hukumar ta Bagwai yace baiwa Doguwa kujerar minista zai taimakawa Kano da  Arewacin Najeriya dama kasa Baki daya, inda ya bukaci sauran 'yan siyasa masu kishi su hada hannu domin tabbatar da bukatar mai matukar muhimmanci.