On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Mataimakin Gwamna A Jihar Edo Ya Fara Kwashe Kayan Offishinsa Daga Gidan Gwamnati

Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shuaibu ya fara mayar da ofishinsa zuwa wani wuri da ke kusa da gidan gwamnati.

Hakan dai  ya biyo bayan janye karar da Shuaibu ya shigar a gaban babbar kotun tarayya a makon da ya gabata domin dakatar da zargin gwamnan jihar Godwin Obaseki na tsige shi daga mukaminsa.

Sabon ofishin yana  lamba 7, Dennis Osadebey Avenue, kusa da gidan gwamnatin jihar ta Edo.

Majiyoyi sun shaidawa manema labarai cewa shugaban ma’aikata ya aike da wasika zuwa ga babbar sakatariya a ofishin mataimakin gwamnan inda ya umarce ta da ta kula da zirga-zirgar ma’aikatan gwamnati da fayil-fayil zuwa sabon ofishin.

An kuma rawaito cewa sabon ofishin   babu wutar lantarki kuma wurin kwanciyar  ruwa ne sannan ofisoshin sunyi kankanta.

Sai dai gwamnatin jihar ta dage cewa sabon ofishin mataimakin gwamnan yana cikin yankin da aka ware a matsayin gidan gwamnati.