On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Mataimakin Shugaban Jam'iyyar APC Ya Sauka Daga Kan Kujerarsa

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC mai kula da shiyyar Arewa maso yamma, Salihu Mohammed Lukman,Ya yi murabus daga kan kujerarsa, biyo bayan yunkurin shugaban kasa, Bola Tinubu na dora tsohon gwmanan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje akan shugabancin jam’’iyyar na kasa.

Idan ba’a manta  ba, Salihu  Lukman  ya fito ‘karara  ya nuna adawarsa  da sanar  da  Ganduje  a matsayin shugaban jam’iyyar  na kasa, Inda  ya  ce  daukar irin wanann mataki abune  da  ya ci karo da  tsarin  yadda  iyayen jam’iyyar  suka  kafa  ta.

Ya kuma baiyana cewar  saukarsa daga kan kujerar  ta fara aiki ne  nan take,  kuma ya dauki matakin ne  sakamakon yanayin da jam’iyyar  ta APC  ta  tsinci kanta  a ciki.

Sai dai  kuma ya sake  jan kunnen shugaban kasa  Bola Ahmed  Tinubu da  ya  guji  yin amfani  da abunda  ya sabawa  tsarin jam’iyyar  wajen tafiyar da harkokinta.