On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Mataimakin Shugaban Kasa Ya Tafi Kasashen Italiya Da Rasha

KASHIM SHETTIMA

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima tashi daga Abuja zuwa kasashen Italiya da Rasha, domin wakiltar shugaban kasa, Bola Tinubu a wasu manyan taruka biyu na duniya da za’a gudanar.

A kasar  Italiya  mataimakin shugaban kasar zai bi sahun sauran  shugabannin kasashen duniya  domin yin taro  akan kirkiro  hanyoyin bunkasa samar da abinci a duniya,  wanda  za’a fara gabatarwa  daga  yau  zuwa  ranar Laraba,  Daga  nan ne kuma mataimakin shugaban kasar  zai  zarce zuwa  kasar  Rasha, domin wakiltar shugaban kasar, kan taron da za’a yi  tsakanin  Rasha da kasashen Afrika  daga ranar  laraba 26 ga watan da muke ciki zuwa Asabar 29 ga watan da muke ciki.

Zai tattauna da  ‘yan siyasa da manyan ‘yan kasuwa a taron da za’a yi  wanda zai mayar da hankali  kan kyautata  alaka tsakanin Rasha da sauran kasashen Afrika, da kuma sauran batutuwa.