On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo Ya Koka Kan Matsalar Aiyukan Ta'adanci A Nahiyar Afrika

Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bukaci shugabannin duniya dasu jingine banbancin dake tsakaninsu tare da yin aiki tare, domin murkushe aiyukan ta’adanci a nahiyar Afrika.

Osinbajo  ya yi wannan kiran ne  a ranar Talata  a yayin wata mukala da aka gabatar a kwalejin  Kings dake birnin London,inda ya koka kan yadda aiyukan ta’addanci  suka yi  kamari a yankin Sahel na Afrika.

Ya baiyana cewar  aiyukan ta’adanci sun haifar da tarin matsaloli,inda  y ace  kamata yayi shugabannin duniya su  fahimci  cewar  matsalar  aiyukan ta’adanci a wani  bangare na duniya, matsala ce  data  shafi dukkanin  ‘yan adam.

Bugu da kari mataimakin shugaban kasa  Yemi Osinbajo ya yi kira  da a kawo karshen rikicin dake faruwa tsakanin kasashen Rasha da Ukrain,tare da yin kira ga kasashen Afrika  dasu tashi haikan wajen  ganin sun dogara da kansu ta bangaren samar da abinci.