On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Matakan Gwamnatin Zamfara Sun Kara Nuna Bukatar Samar Da ‘Yan Sandan Jahohi A Najeriya - Akeredolu

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa kiran da gwamnatin jihar Zamfara ta yi na al’umma su dauki makamai su kare kansu hakan ya sake jaddada bukatar kafa ‘yan sandan jihohi domin dakile ayyukan ta’addanci a sassan kasar nan.

Gwamna Akeredolu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata ta hannun mai taimaka masa kan  ayyuka na musamman Dr Doyin Odebowale.

Ya ci gaba da cewa kiran da gwamnatin jihar Zamfara ta yi na neman ‘yan kasa su mallaki bindiga ya nuna rashin gamsuwa da tsarin tsaron kasa a halin yanzu.

 Odebowale ya kuma yi tir da yadda gwamnatocin jihohi ke gaza kare al’ummarsu dake fama da hare-haren ‘yan bindiga.

Ya yaba da jajircewar Gwamna Bello Matawalle a yunkurinsa na tunkarar kalubalen tsaro a jihar Zamfara ta hanyar amfani da matakan da suka dace.