On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Matasan Da Suka Kai Hari Da Sace Kayyaki Da Sunan Murnar Zabe Sun Shiga Hannun Rundunar 'Yan Sanda A Kano

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta kama wasu mutane 29 da ake zargi da kai hari gida da ofisoshin fitaccen mawakin siyasa Dauda Adamu Abdullahi da akafi sani da Rarara da kuma sakatariyar jam’iyyar APC a jihar.

Rundunar ‘yan sandan ta ce ‘yan barandan da suka kai hari gidan Rarara da ofishinsa da ke titin gidan Zoo sun yi awon gaba da kayayyaki na miliyoyin Naira.

Sun kuma kai hari kan shagunan kasuwanci guda hudu na mutane daban-daban.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanya wa hannu, ta ce wasu gungun bata gari sun kai hari tare da lalata wasu sassan ofishin sakatariyar jam’iyyar APC na jihar Kano da ke Hotoro.

Yanzu haka dai rundunar ‘yan sanda  ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.