On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Matasan Da Suka Kammala Horo Kan Dabarun Tsaro A Kano Na Neman Daukin Gwamna Abba

Matasan da suka kammala makarantar koyar da dabarun tsaro dake garin Zakirai a karamar hukumar Gabasawa, na rokon daukin Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya samar musu da guraben ayyukan yi domin tallafa wa harkar tsaro da zaman lafiya a Jihar ta Arewa maso Yammacin Najeriya.

Shugaban kungiyar daliban, Kamalu Auwalu Ibrahim, wanda ya yi wannan roko a madadin daliban da suka kammala karatu a makarantar, ya ce a makarantar an koyar da su dabarun tsaro tare da alkawarin za a ba su ayyukan yi bayan sun kammala horon.

Auwalu ya kara da cewa sama da matasa 200 sun samu horo  da dabarun tsaro, wanda zai taimakawa kokarin hukumomi a fannin tsaro da masu ruwa da tsaki wajen dorewar  zaman lafiya.