On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Matatar Mai Ta Dangote Na Shirin Fara Tace Man Dizal Da Man Jirgin Sama A Farkon Shekarar 2024

Matatar mai ta Dangote tace zata fara samar da man dizal da na jiragen sama daga watan Janairun 2024, yayin da ake samu jinkirin tace man Fetur saboda rashin samun danyen mai.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne dai mahukuntan matatar man Dangote suka tabbatar da samun ganga miliyan daya na danyen mai wanda zai bada damar fara aikin  tacewa a matatar.

Sai dai wani jami’in kamfanin ya shaida wa manema labarai a ranar Lahadi cewa, abin da ‘yan Najeriya za su yi tsammani a watan Janairu shi ne man dizal da na jiragen sama domin Fetur  yana bukatar akalla ganga miliyan shida na danyen mai domin a fara tacewa, amma  ganga miliyan daya kacal aka samu.

Idan za’a iya tunawa Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC Limited ya bayyana a ranar 3 ga Nuwamba na 2023, cewa zai samar da ganga miliyan shida na danyen mai ga matatar Dangote.

Sai dai duk da Alkawarin hakan bata samu ba.