Dan wasan gaba na kasar Faransa, Kylian Mbappé, ya kafa sabon tarihi bayan ya zama wanda ya fi kowa zura kwallaye a tarihin gasar cin Kofin Duniya ta FIFA, inda yawan kwallayensa ya kai 22.
Wannan nasara ta sa Mbappé ya haura saman jerin masu yawan kwallaye a gasar ta maza, inda ya karya tarihin da aka dade ana rike da shi.
Har ila yau, kyaftin din na Faransa ya kara fadada gibin da ke tsakaninsa da sauran 'yan wasa a fafatawar lashe kyautar wanda ya fi kowa zura kwallaye a gasa guda ta Golden Boot, bayan ya kai kwallaye 10 a gasar ta bana, wanda ya ba shi tazarar kwallaye biyu a kan wanda ke binsa.
Mbappé ya cimma wannan tarihi ne a wasan neman matsayi na uku tsakanin Faransa da Ingila, lamarin da ya kara tabbatar da matsayinsa a matsayin daya daga cikin fitattun masu zura kwallaye a tarihin gasar Kofin Duniya ta FIFA.
A wannan wasa dai Inila ta samu galaba akan Faransa da ci 6 da 4 domin lashe sarkar tagulla a gasar ta bana.
Comments
Add a comment