Jagoran cikin fili na kungiyar kwallon kafa ta ƙasar Faransa, Kylian Mbappe, ya bayyana wata Sanata daga Paraguay, Celeste Amarilla, a matsayin wadda ba ta cancanci muƙaminta ba, bayan ta yi masa kalaman wariyar launin fata a shafukan sada zumunta sakamakon wasan zagaye na biyu na Gasar Kofin Duniya da Faransa ta doke Paraguay da ci 1-0.
Mbappe ya mayar da martani ne ta shafinsa na X, inda ya ce Amarilla ba ta wakilci ƙasar Paraguay ba, yana mai cewa al'ummar ƙasar sun nuna ƙwazo da mutunci a gasar, amma kalamanta na nuna rashin sani da kuma nuna wariyar launin fata.
Sanatar ta bayyana Mbappe da kalamai masu cin mutunci, inda ta kira shi "ɗan Kamaru da aka yi wa mulkin mallaka wanda ya yi kamar ɗan Faransa ne", tare da zarginsa da girman kai da kuma tsoro yayin wasan.
Lamarin ya haifar da suka a Faransa, inda Ministar Wasanni ta ƙasar, Marina Ferrari, ta bayyana kalaman a matsayin abin kunya kuma maras karɓuwa, musamman kasancewar sun fito daga wata 'yar siyasa. Mbappe, wanda mahaifinsa ɗan asalin Kamaru ne, shi ne ya jefa kwallo a raga a bugun daga kai sai tsaron gida da ta bai wa Faransa nasara, kuma yanzu ƙasar za ta kara da Morocco a wasa na matakin ukun karshe ranar Alhamis.
Madame Celeste Amarilla,
— Kylian Mbappé (@KMbappe) July 6, 2026
Vous êtes une femme méprisable et indigne de sa fonction.
Vous ne représentez pas le Paraguay, ce pays qui a transpiré la passion et l’honneur tout au long de la compétition. Par votre inconscience et votre racisme décomplexé, le monde entier a déjà… pic.twitter.com/EnYmgQXvPL
Comments
Add a comment