On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Messi Zai Yi Bankwana Da PSG A Ranar Asabar

MESSI

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain PSG Christophe Galtier ya tabbatar da ficewar Dan wasa Lionel Messi daga kungiyar, Inda ya yi fatan magoya bayan kungiyar za su yi masa bankwana na musamman wasansa na karshe da kungiyar zata buga a ranar Asabar.

Wasan da kungiyar  zata  yi  da   Clermont zai kawo karshen zaman Messi na tsawon shekaru biyu a  kungiyar  ta   PSG.

Da alama dai babu  rade-radin da ake  yi  na cewar  dan wasa  Messi zai koma  tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona.

Ana  tsammanin  tauraron dan wasan zai koma  saudiyya da  buga tamaula   , inda zai bi sahun abokin hamaiyyarsa  a kwallo Cristiano Ronaldo a kan yarjejeniyar miliyoyin daloli.