On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Milyan 560 Gwamnatin Taraiyya Ta Kashe Wajen Kwashe 'Yan Najeriya Zuwa Masar A Mota

onyema

Gwamantin taraiyya ta ce ta kashe zunzurutun kudi har naira milyan 560 domin jigilar ‘Yan Najeriyan da suka makale a kasar Sudan ta cikin motocin safa, zuwa wuraren da suke da amince da za’a iya dauko su ta cikin jirgin zuwa gida Najeriya, biyo bayan yakin da ya barke a kasar ta Sudan.

Ministan harkokin kasashen Waje  Geofrrey  Onyeama  ne  ya  baiyana haka a ranar Laraba , Lokacin da yake amasa  tambayoyin  manema  Labarai na  fadar shugaban kasa a Abuja,  Ya kuma kara da cewar  babu wani Dan Najeriya  da  ya rasa  ransa  saboda  yakin da ake yi a kasar.

Ya kara da cewar za’a dauki tsawon kwanaki biyu kafin kammala  kwashe  ‘Yan  Najeriyar da suka makale a kasar  ta Sudan,  Bugu da kari  ya  ce  da zarar  an kammala kaisu kasar  Masar, za’a yi tsare-tsaren da suka dace  domin dauko su ta cikin jirgi zuwa gida  Najeriya.

Ya kuma cewar  za’a bayar da kulawa ta musamman ga Mata da kananan yara  kafin a kaiga  saka  jami’an  Diflomasiyyar  kasar  nan wadanda  suma  suna cikin  mutanen da za’a kwaso.