On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Ministan Shari'a Ya Angwance Da 'Yar Shugaban Kasa.

MINSITAN SHARI'A ABUBAKAR MALAMI

A ranar Juma’a ne, Babban Lauyan gwamnatin taraiyya kuma ministan shari’a na kasa, Abubakar Malami, Ya angwance da amaryarsa Nana Hadiza, Wadda ta kasance ‘ya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kakakin shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya tabbatarwa da manema Labarai cewa Ministan shari’ar ya aure yar shugaban kasar a jiya, kuma anyi bukin ne cikin sirri a fadar shugaban kasa dake Villa Abuja.

Hajiya Hadiza Buhari ta kasance ‘ya ga tsohuwar matar shugaban kasa, sannan kuma a yanzu itace ta ukku a jerin matan ministan shari’ar na kasa, kuma rahotanni sun tabbatar da cewa a baya ta taba yin aure harma tana da yara  shida.