On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Ministan Tsaro Ya Roki 'Yan Najeriya Su Taya Shi Da Addu'a.

BADARU

Yayin da ake tsaka da fuskantar kalubalen tsaro a wasu sassan kasar nan , Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da yi wa gwamnati mai ci addu’a, musamman masu rike da mukaman kula da tsaron kasa.

Badaru, wanda ya yi wannan roko ne a  ofishinsa da ke Abuja a lokacin da ya karbi bakuncin wata  tawaga ta musamman  daga Ja gawa karkashin jagorancin gwamnan jahar, Malam Umar Namadi, ya ce irin sarkakiyar kalubalen tsaro da ake fuskanta a Najeriya, Babu abunda mutum  yake bukata sai addu’o’in samun nasara.

A cewarsa, duk da cewa aikin da ke gabansu na da yawa, amma sun kuduri aniyar shawo kan kalubalen da ake fuskanta, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su mara musu baya ta kowane fanni da suka hada da yi masu  addu’o’i domin ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.

Shima  a nasa jawabin  gwamnan jahar Jigawa, Umar Namadi, wanda ya jagoranci sarakunan gargajiya da  malaman addini da  ‘yan kasuwa da masu rike da mukaman gwamnati da suka fito daga ja har  a yayin ziyarar , ya ce sun je wajen ministan tsaron ne  domin taya  shi murna tare da ba shi tabbacin samun  goyon bayansu a kowane lokaci.