On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Muna Kashe Naira Milliyan 66 Kudin Gudanarwa Duk Wata A Kano - Shoprite

Mamallaka shahararren kantin sayar da kayayyaki na Shoprite, sun bayyana tsadar kudin gudanarwa amatsayin dalilin da ya sa zai fice tare da  kawo karshen ayyukansa a jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa Shoprite na biyan Naira milliyan 66 a matsayin haya a Ado Bayero Mall duk wata.

Wata takardar da mahukuntan kantin suka sanya wa hannu, Shoprite ya ce wannan baya ga kudin wutar lantarki mai zaman kansa da suke biya daga Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano KEDCO, da kuma kudin mai da kuma kula da janaretonsa.

Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya babban kanti ya bayyana aniyarsa ta daina aiki a reshensa na Kano dake Arewa maso Yammacin Najeriya daga ranar 14 ga watan Janairun 2024.