On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Mutane 10 Sun Kone Sakamakon Fashewar Wata Tankar Mai A Jos

TANKA

kimanin mutane 10 ne suka kone, A yayin wasu da dama kuma suka jikkata bayan da wata tankar mai dauke da mai ta fashe a birnin Jos na jihar Filato.

Rahotanni sun baiyana cewar   tankar ta fadi ne da misalin karfe 12 da Rabi na dare sannan ta kama  da wutar   yayin da take  kokarin yin kwana  a Angwan Rogo, daura da mahadar  titin  zuwa Bauchi.

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, DSP, Alfred Alabo ya fitar, ya ce  mutane 10  ne suka kone, kuma  har  yanzu ba’a kaiga  tantance sub a.

Ya ce ana kokarin dawo da zirga-zirgar ababen hawa a   wajen da abun ya  faru,  tare da kokarin gano  wadanda abun ya ritsa  dasu.

Sai dai  shaidun gani da ido sun ce sama da gawarwaki 20 ne  suka  kone kurmus, yayin da wasu 12 kuma aka kwashe su zuwa dakin ajiyar gawa.