On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Mutane 10 Sun Mutu Yayin Da 15 Suka Jikkata A Sakamakon Hadarin Mota A Jihar Filato

JAMI'AN HUKUMAR KARE AFKUWAR HADURRA

Hukumar kare afkuwar hadurra ta kasa reshen jihar Filato, Tace mutane 10 ne suka rasa rayukansu a yayin da wasu 15 suka jikkata a yayin wasu hadurra biyu wanda ya ritsa da wasu motoci bakwai akan hanyar Jos zuwa Bauchi.

Kwamandan Hukumar Alphonsus Godwin ne ya baiyana haka a ranar Alhamis a birnin Jos, Yace abun alhinin ya ritsa da wata babbar mota da kuma kananan motoci 6.

Yace  Babbar  motar  ta kwacewa  direbanta  wanda bai kai munzali ba, wanda  hakan yasa  tayi taho mu gama da motoci, al’amarin da yayi sanadin faruwar hadurran.

Daga nan sai ya shawarci masu manyan motoci dasu rika tabbatar da lafiyar ababen hawansu, tare da bibiyar direbobin, da kuma dena  Saka  kananan yara  tuki.