On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Mutane 130 Sun Kamu Da Cutar Mashako A Jihar Kano

MASHAKO

Gwamnatin jihar Kano ta samar da wasu cibiyoyin kula da masu cutar Mashako guda ukku a jihar nan, a yayin da wadanda suka kamu da cutar yah aura 130.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Abubakar Yusuf ne ya baiyana haka a ranar Alhamis, Y ace gwamnati ta dauki matakan da suka da suka dace domin dakile bazuwar  cutar.

Kazalika  y ace  zuwa ranar  Litinin mutane sama 130 ne aka kwantar akan gadon asisbiti saboda kamuwa da cutar a  yayin da take ci gaba da karuwa.

Kazalika  kwamishinan lafiya  na jihar  kano ya  koka  da cewar jiha  kamar  kano bai kamata ace  tana  fama  da irin wannan cuta  ba, inda  ya zargi  tsohuwar  gwamnati  da rashin yin rigakafi  ga jama’ar  jihar nan.