On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Mutane Biyu Sun Mutu A Kano Sakamakon Mamakon Ruwan Sama

Mutane biyu ne suka rasa rayukan su sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi, a daren Asabar zuwa wayewar garin Lahadi a jihar Kano.

Mutanen sun hada da Yahya Zakariyya mai shekaru 27, da kuma Nasiru Adam mai shekaru 55, inda kuma ruwan sama yayi awon gaba da ababan hawansu, a hanyar su komawa gida daga wajen aiki, a kan titin Kanzu dake karamar hukumar Dala.

Daya daga cikin ‘yayan wanda ya rasun, wanda ya zanta da Arewa radio, tare da tabbatar da faruwar lamarin, yace mahaifin nasa mai shekaru 55, sun samo shine a safiyar  ranar Litinin inda ake cigaba da ceton 

Duk da cewa har yanzu ba a gano daya mamacin ba, har zuwa hada wannan lokaci da muke hada  rahoton.