On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Mutane Biyu Sun Mutu Yayin Da Wasu Sukayi Batan Dabo A Sakamakon Hadarin Kwale-Kwale A Jihar Jigawa

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a wani hadarin kwale-kwale da ya faru a karamar hukumar Ringim.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu, shine  ya tabbatar da faruwar lamarin  ta cikin  wata sanarwa daya fitar  a  Dutse babban birnin jihar. Shiisu ya ce kwale-kwalen mai dauke da fasinjoji 13  suna  kan hanyarsu  ta zuwa ziyarar jaje, lokacin daya kife bayan da bugi wani abu.

Ya bayyana cewa biyu daga cikin fasinjoji bakwai dake cikin jirgin da suka rigamu gidan gaskiya sun hada  da , Bara’atu Garba da Mahmud Surajo .

A cewarsa, an mika gawarwakin mutane ga iyalansu domin yi masu sutura yayin da sauran mutane biyar ke samun kulawa a asibiti. Ya kara da cewa har yanzu ba a ga ragowar sauran mutane shida da suka nutse a cikin ruwan ba.

More from Labarai