On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Mutane Hudu Sun Mutu Saboda Wata Arangama Tsakanin Ayarin Gwamnan Jihar Kaduna Da 'Yan Shi'a

NASIR EL-RUFAI

Mutane hudu ne ake fargabar sun mutu a sakamakon wata arangama da aka yi tsakanin jami’an tsaro dake raka tawagar gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i da wasu ‘yan kungiyar Shi’a a yankin Bakin Ruwa dake jihar Kaduna a jiya.

Ayarin  gwamnan   sunyi  taho mugama  da  mabiya  mazhabar  ta shi’a ne a  lokacin da suke  gudanar da tattakin  da suka  saba  yi  duk mako a  kusa  da kan babbar  hanyar  Nnamdi Azikiwe  da karfe  4 da mintina 15  na  yammaci, a lokacin da gwamnan yakai  wata ziyara  yankin.

Daya  daga cikin ‘yan uwan  wadanda suka rasa ransu mai suna   Yusha’u  Muhammed, Dan  uwan nasa  da  ya gamu da ajalinsa  ba, Direban motar  haya  ne   ba  ‘Dan Shi’a  ba  ne,  Sai dai ya  rasa  ransa  ne a  sakamakon  wani harsashin  bindiga  da  ya same  shi.

Wani wakilin  kungiyar  ta shi’a a  jihar  Kaduna,  Abdullahi  Usman ya  fadawa  jaridar  Daily Trust  cewar, dukkanin wadanda  suka  rasa  ransu  ba ‘yan shi’a  ba ne, Inda  ya  baiyana  cewar  direbobin motar  haya  ne  da suka  tsaya a  wata  tashar  mota  dake kusa  da wajen da abun ya faru.

Kakakin rundunar  yansandan jihar  DSP  Mohammed  Jalige  ya  ce  a yanzu haka ana  kan gudanar da bincike,kuma rundunar  zata yi cikakken jawabi a nan gaba  kadan.