On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Mutane Sama Da 10 Sun Mutu A Wani Gidan Ca-ca Bayan Da Gobara Ta Tashi

GIDAN CA-CA A CAMBODIA

Akalla mutane sama da goma ne suka mutu a sakamakon tashin wata gobara a wani gidan Caca dake jikin wani otal dake kasar Cambodia akan iyakar kasar da Thailand.

Jami’an yansanda  sun baiyana cewa daruruwan mutane ne ke a cikin ginin  lokacin da gobarar  ta  tashi a  gidan Cacar  wanda ke a garin Poipet a ranar Larabar data gabata.

Wasu faya-fayan bidiyo da suka karade  shafukan sada zumunta  sun nuna  yadda  mutane   suka rika dirowa  daga saman bene, A yayin da kafofin yada labaran yankin suka ce da yuyuwar a samu karuwar mutanen da suka mutu.