On Air Now

ZANGON SAFIYAR LAHADI

5:00am - Noon

Mutane Sama Da 40 Sun Mutu Sakamakon Arangama Tsakanina 'Yan Ta'adda Da 'Yan Sa kai A Jihar Katsina

Masu Garkuwa

Wata bata kashi da aka yi tsakanin mayakan tada kayar baya da kuma ‘yan Sa kai a jihar Katsina, ta yi sanadin mutuwar mutane kimanin 41.

Mai magana da yawun rundunar  yansandan  jihar  Gambo Isah ne ya  tabbatar da haka ga manema labarai a ranar juma’a.

Ya  ce  Kungiyoyin ‘yan sa kan da suka fito daga wasu kauyuka  goma sha daya a karamar hukumar Bakori sun  tunkari  ‘yan ta’adda da zummar  su kwato dabbobinsu da suka sace masu.

Lamarin ya faru ne  kwana daya  bayan da  ‘Yan ta’addar  masu  yawan gaske  suka rika yin harbi bayan wani hari da suka kai gidan wani mai suna Alhaji Muntari  dake unguwar Audu Gare a karamar hukumar  ta Bakori, inda suka sace  shanu hamsin tare da Tumaki  Talatin.