On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Mutane Sama Da Dubu Biyu Sun Mutu Saboda Girgizar Kasa A Turkiya Da Syria

HOTON GIRGIZAR KASA A TURKIYA

A yanzu haka yawan mutanen da suka rasu a sakamakon ibtila’in girgizar kasa data faru a kasashen Turkiya da Syria ya karu zuwa dubu biyu da dari ukku a cikin kwana daya da faruwar al’amarin.

Girgizar kasar mai karfin gaske  ta afkawa kasashen ne  da  asubahin jiya , a  yayin da har yanzu  jami’an bada agaji ke cigaba da  zakulo  gawarwarkin mutanen da suka mutu.

Masu aikin ceto sun yi amfani da manyan kayan aiki da hannayensu  wajen zakulo  baraguzan gine-gine domin  neman wadanda suka tsira, wanda  a wani lokacin ake  jiyo  sautin neman  temako a karkashin baraguzan  gine-gine.