On Air Now

ZANGON RANAR ASABAR

Noon - 6:00pm

Mutane Shida Sun Mutu A Sakamakon Mamakon Ruwan Sama A Jihar Jigawa

AMBALIYAR RUWA

Hukumar Bada agajin gaggawa ta jihar Jigawa SEMA, ta ce mutane shida ne suka mutu sakamakon mamakon ruwan sama da aka samu a karamar hukumar Kafin-Hausa dake jihar.

Shugaban hukumar  bada agajin gaggawa ta jihar, Yusuf Sani, ya  baiyanawa  manema labarai cewa mutane 65 ne suka samu raunuka  a sakamakon mamakon ruwan saman da aka samu   a ranar Talata.

Sani ya ce jami’an  bada agajin gaggawa na gwamnatin jihar da kuma na tarayya suna tantance irin barnar da mamakon ruwan sama ya haifar, Ya kara da cewa, har yanzu ba a tantance adadin gidaje da kadarorin da  aka yi asarar su  ba, a sakamakon  ibtila’in da aka samu.

Bugu da kari ya bukaci  wadanda mamakon  ruwan  ya  raba  da muhallansu da su zauna tare  da  ‘yan uwansu har  zuwa  lokacin da za’a samar masu da matsugunni.