On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Mutane Takwas Sun Kone A Lokacin Da Suke Dibar Man Wata Tankar Mai Data Fadi

Hukumar kare afkuwar haddura ta kasa, Ta tabbatar da mutuwar wasu mutane takwas, lokacin da suke dibar wani Man fetir na wata tankar mai data fadi a matsayin ganima, a kusa da babbar hanyar ore zuwa Benin a jihar Ondo.

A baya  an ruwaito cewar Mutane da dama ne  suka mutu  cikinsu  hadda  wata mata mai dauke da juna biyu sakamakon ibtila’in na ranar Lahadin data  gabata,To sai shugaban  hukumar kare afkuwar  haddura  ta kasa  reshen jihar, Ezekiel Son, Y a ce  mutane  takwas  ne suka  kone.

Ya ce tankar  wadda  babu wata  lamba a jikinta  ta kwacema  direbanta ne sakamakon gudun wuce sa’a  da yake yi,  Kazalika  ya  ce  daga bisani tankar  ta kama da wuta lamarin da yayi sanadin mutuwar mutane  takwas a lokacin da suke kwasar  man  a matsayin ganima.