On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Mutanen Da Suka Gamu Da Tangardar Na'ura Zasu Sake Rubuta Jarabawar Jamb

JAMB

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB zata sake baiwa wadanda suka gamu da kalubale na tangardar na’ura a lokacin rubuta jarabawar UTME a ranar Talata, damar sake rubuta jarabawar.

Mai magana da yawun hukumar, Febian Benjamin ne  ya baiyana haka a Abuja  jim kadan bayan wani taron gaggawa da jami’an hukumar suka gudanar, inda aka tattauna kan kalubalen da aka fuskanta game da rubuta jarabawar a rana ta farko.

Ya  ce  kimanin cibiyoyi  100  daga cikin 708  da aka rubuta jarabawar ne suka fuskanci kalubale na tangardar na’ura  wanda  ya hana  mutane rubuta  jarabawar.

A saboda  haka  y ace duk wanda yake da irin wannan matsala  zai sake fitar  da sabon Slip  na  rubuta  jarabawar  a  yau,domin sanin lokacin da zai sake  zama  jarabawar  da kuma wuri.