On Air Now

Off Air

Midnight - Noon

Mutanen Da Suka Mutu Sakamakon Wani Hari A Jihar Filato Ya Karu Zuwa 85

Adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai na ranar Talata a karamar hukumar Mangu ta Jihar Filato ya karu zuwa 85, yayin da ake ci gaba da neman wadanda suka bace a yankunan da lamarin ya shafa.

Shugaban kungiyar ci gaban   yankin, Joseph Gwankat ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Laraba, Jim  kadan bayan   kammala wani  taron tsaro da aka gudanar a fadar sarkin garin Mangu.

Gwankat ya baiyana  cewar  wandanda   ake zargin  sun kai harin  makiyaya ne, lamarin da ya yi  sanadin kashe-kashen da aka samu da kona gidaje  tare  kuma  kuma lalata gonaki a yankunan nasu.

Daruruwan  Mata ne  suka  zagaye   fadar sarkin a lokacin da ake  gudanar da taron, a wani mataki na nuna bacin ransu  kan yawan hare-haren  da ake kai masu.