On Air Now

ZANGON MARAICE

3:00pm - 8:00pm

Mutum 17 Sun Raunata Yayinda Aka Kaiwa 'Dan Takarar Sanata Na Jam'iyyar APC Hari A Jihar Kano

Akalla mutane 17 ne suka ji raunuka daban-daban a ranar Asabar yayin da wasu ‘yan daba suka kai hari kan ayarin motocin yakin neman zaben dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Abdussalam Abdulkarim a kauyen Gayawa da ke jihar Kano.

Wani ganau ya ce dan takarar mai da ake kira AA Zaura ya tsallake daga harin da  kyar ba tare da samun wata matsala ba, inda aka lalata motocin yakin neman zabensa sama da 10.

Mai taimakawa Zaura kan harkokin yada labarai, Ibrahim Mua’azzam, ya ce al’amarin ya faru ne a lokacin da suke dawowa daga Ta’aziyya.

A halin da ake ciki, Darakta Janar na yakin neman AA Zaura, Yahaya Adamu Garin Ali, a cikin korafin da ya shigar ranar 17 ga watan Disamba ya bukaci kwamishinan ‘yan sandan da ya gudanar da cikakken bincike.

More from Labarai