On Air Now

ZANGON RANA

10:00am - 3:00pm

Mutum 2 Sun Mutu Sanadiyar Rushewar Katanga A Babban Birnin Najeriya Abuja

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta babban birnin tarayya Abuja, FEMA, ta tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da ceto wasu mutane hudu a wata katanga da ta rushe a unguwar Ademola Adetokunbo Crescent dake Wuse II a Abuja.

Babban daraktan hukumar ta FEMA, Abbas Idriss, ya ce wani bangare na ginin ya fado akan masu sana’ar hannu da ke aiki a wurin.

Idriss ya ce hukumar ta samu nasarar ceto mutane shida daga baraguzan ginin yayin da hudu ke kwance a asibiti, biyu kuma suka mutu.

Ya danganta al’amarin da tsawaita ginin da aka yi  wanda a karshe ya rushe kan masu sana’ar.