On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

Mutum 5 Sun Mutu Yayinda Aka Ceto Mutum 4 Sanadiyar Kifewar Kwale-kwale A Jigawa

Akalla mutane biyar ne aka tabbatar sun mutu sakamakon hatsarin jirgin kwale-kwale a kauyen Martaba da ke karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa CP Sale Tafida shine ya tabbatar da faruwar al'amarin ta cikin wata sanarwa da  jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Lawan Shiisu Adam ya fitar ga manema labarai a Dutse.

A cewar sanarwar, a ranar Juma’a, 2 ga Satumba, 2022, wani kwale-kwalen  ya kife da fasinjoji tara (9).

Al'amarin  ya faru ne a kauyen Martaba karamar hukumar Gwaram ta jihar Jigawa, yayin da fasinjojin ke komawa gida bayan kammala sallar Juma’a.

Bayan samun rahoton, an  tura  da tawagar ‘yan sanda zuwa wurin.

An kubutar da hudu (4) a raye daga cikin fasinjojin da suka hadar da Barkeji  mai shekara 60, da wasu mutum uku (3) duk a kauyen Martaba.

Yace bisa taimakon masu ruwa da tsaki anyi nasarar  tsamo gawarwaki biyar (5) da suka hadar da  Lukateru dan shekara  60 da  Musa mai shekara 50 da Sale mai shekara 50 da Alhaji Shuaibu dan  shekara 60 da Dogo mai  shekara 50  dukkanninsu 'yan  sansanin makiyaya na Darazau da ke jihar Bauchi.

An mika gawawwakin ga ’yan uwansu daga nan Kwamishinan ya jajantawa ‘yan uwan.

Ya kuma yi addu'a ga wadanda suka rasu.