On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

Mutum Guda ya Mutu, Wasu sun Bace a Hadarin Jirgin Ruwa a Jigawa

Akalla mutum daya ya rasa ransa yayin da wasu da dama suka bace sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya afku a kauyen Malamawa da ke 'Yan Dutse a karamar hukumar Ringim ta Jihar Jigawa.

Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne a ranar Lahadi lokacin da wani kwale-kwale dauke da kimanin fasinjoji 40, wadanda akasarinsu mata da kananan yara ne, ya kife yayin da yake tsallaka wani tafkin ruwa a yankin.

A cikin wata sanarwa da Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Jihar Jigawa, SP Shi'isu Lawan Adam, ya sanya wa hannu, rundunar ta tabbatar da afkuwar lamarin, tana mai cewa an gano gawar mutum daya zuwa yanzu, yayin da ake ci gaba da aikin ceto domin gano sauran fasinjojin da suka bace.

Kakakin rundunar ya ce jami'an tsaro, masu aikin ceto da kuma masu sa kai sun bazama domin laluben ruwa da kuma ceto wadanda hatsarin ya rutsa da su, yana mai tabbatar da cewa za a cigaba da aikin har sai an gano dukkan fasinjojin.

Haka kuma, Majalisar Masarautar Ringim ta tabbatar da afkuwar hatsarin a cikin wata sanarwa, inda ta bayyana cewa lamarin ya yi sanadiyyar rasa rayuka, sai dai ta ce har yanzu ana cigaba da tantance adadin wadanda suka mutu da kuma wadanda aka ceto.

Majiyoyin yankin sun shaida cewa mazauna garin sun hada kai da jami'an tsaro wajen gudanar da aikin ceto, yayin da shugabannin gargajiya suka bukaci jama'a su kwantar da hankulansu tare da bai wa masu aikin ceto cikakken hadin kai.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomi ba su fitar da cikakken adadin wadanda hatsarin ya rutsa da su ba, yayin da ake cigaba da gudanar da bincike kan musabbabin hatsarin da kuma laluben ruwa domin gano sauran fasinjojin.

Hatsarin kwale-kwale na cigaba da zama babban kalubale a yankunan da ke makwabtaka da koguna a Arewacin Najeriya, musamman a lokacin damina, lamarin da ya sa masana ke ci gaba da kira ga masu ruwa da tsaki su tabbatar da amfani da rigunan kariya, duba lafiyar kwale-kwale akai-akai da kuma hana daukar fasinjoji fiye da adadin da aka kayyade domin rage yawan irin wadannan hadurra.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Thundery shower

    High: 35°C | Low: 23°C