On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

Na Dauki Kwana Biyu Ban Rintsa Ba Domin Nasarar Akpabio

SANATA BAMIDELE

Daraktan yakin neman zaben Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa na goma, Sanata Opeyemi Bamidele ya ce sanatocin da ke muradin ganin Godswill Akpabio ya samu nasara, sun hallara zauren majalisar dattawa tun da karfe 4 na Asubahin jiya, domin dakile irin abunda ya faru a zaben shugaban majalisar dattawa na shekarar 2015.

Idan ba’a manta  ba a shekarar  2015,  Sanatocin dake goyon bayan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, Suka yi zaman dirshan a zauren majalisar dattawan domin tabbatar da nasarar  tsohon gwamnan jihar Kwara a  matsayin shugabansu, A yayin da ragowar sanatocin ke ganawa da  shugaban kasa Buhari a daidai lokacin da aka rantsar da sabon shugabancin majalisar.

Da yake jawabi a yayin wata liyafa da aka shirya masa domin murnar komawarsa zauren majalisar dattawa a karo na biyu, Sanata Bamidele dake wakiltar Ekiti ta tsakiya, Ya  ce  ya dauki tsawon kwanaki biyu batare da ya rintsa ba,  domin tabbatar da nasarar  Sanata Godswill Akpabio.

Comments

Add a comment

Log in to the club or enter your details below.

A Biyo Mu a Shafukan Sada Zumunta

Today's Weather

  • Kano

    Sunny intervals

    High: 37°C | Low: 23°C