On Air Now

ZANGON BARKA DA SAFIYA

5:00am - 10:00am

NAFDAC Ta Bukaci Jama'a Su Dena Yin Amfani Da Maganin Karin Kuzari Na Prime Prime Zen Black

PRIME ZEN

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC Ta ja kunnen jama’a game da yin amfani da wani maganin karin kuzari mai suna Prime Zen Black dake yawo a kasuwanni.

Hukumar  ta  yi jan hankalin ne  ta cikin wata sanarwa  mai dauke dasa  hannun shugabar  hukumar Mojisola Adeyeye wadda aka rabawa manema labarai a Abuja.

Ta ce  ana yin maganin ne a  kasar  Amurika  kuma akwai sinadarai  masu cutarwa  a  cikinsa.