On Air Now

Off Air

Noon - 6:00pm

NAFDAC Ta Ce Akwai Karancin Ingantattun Wuraren Ajiyar Magani A Jihar Kano

NAFDAC

Hukumar kula da ingancin Abinci da Magunguna ta kasa NAFDAC ta baiyana fargabar ta kan lalacewar mafi akasarin wurin magani da ake dasu a jihar Kano.

Babban  jami’in hukumar  reshen jihar Kano, Kasim Idrisa  ne ya baiyana haka lokacin  da  yake karin haske  kan aiyukan hukumar  a zangon farko na shekarar  bana.

Ya kara da cewar  hukumar zata  tursasawa  daukacin masu harkar  magani a jihar kano  komawa  sabuwar kasuwar saida magani ta zamani  wadda aka saka mata dukkanin kayan zamani da ake bukata  dake kan titin zuwa Zariya ,  domin samun saukin bankado  jabun  maguguna  da ake  hada-hadarsu.

A  cewarsa  sama  da kanfanoni 35  a nan jihar  kano aka  daukin matakin ladabtawa akansu  a wannan zangon  sakamakon  aikata lefuka,  wanda  ya shafi  yin amfani da wurin ajiyar magani maras inganci da  kuma rashin bin  ka’idojin hukumar  ta  NAFDAC.