On Air Now

Off Air

Midnight - 5:00am

NAFDAC Ta Gargadi Mata Masu Amfani Da Mayukan Canza Launin Fata

Mayukan canza launin fata

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC taja kunnen jama’a dasu yi hattara kan wasu mayukan canza launin fata dake yawo a kasuwanni, wanda ta baiyana da cewar zasu iya haddasa samun barkewar wata annoba.

Hukumar ya baiyana haka ne a yayin wani taron karawa juna sani da ta shirya kan illolin yin amfani da mayukan canza launin fata, wanda aka  gabatar a Fatakwal  babban birnin jihar Ribas.

Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye  ta koka kan illolin dake tattare da yin amfani da irin wadannan mayuka ,inda  ta bukaci matan kasar  nan dasu kasance masu tinkaho da  ainihin launinsu na fata  da suke dashi.