On Air Now

ZANGON DARE

8:00pm - Midnight

NAHCON Ta Fitar Da Farashin Kujerar Hajjin 2023

An sanar da kudin kujerar aikin hajji a Najeriya ga maniyyatan 2023

Shugaban Hukumar, Alhaji Zikirulla Kunle Hassan shi ne ya sanarwa manema labarai hakan, a yayin wani kwarkwaryar taron da hukumar ta gudanar da shugabannin hukumomin jin dadin alhazai na jahohi wanda ya gudana a ranar Juma'a.


Zikirulla yace karin kudin kujerar aikin Hajin na 2023 ya faru ne sakamakon tashin farashin canjin Dala  da kuma karin kudin ayyukan kula da alhazai da hukumomin Saudi Arabia suka yi

Shugaban ya kuma sanr da ranar 21 ga watan Afurilu a matsayin ranar karshe da hukumomin da abun ya shafa zasu sanyawa hukumar aikin hajin ta kasa kudaden Maniyyatan da zasu ta shi a jahohinsu ko kuma kamfanoninsu.

Da yake karin haske kan yadda biyan kudaden zai kasance tsakanin shiyyoyi ko jahohin Najeriya, Kunle ya ce Jahohin dake yankin Arewa maniyyatansu zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da sha tara (2,900,19,000.00) 

Sai kuma jahohin da zasu tashi ta jahohin Maiduguri da Yola, su kuma maniyan zasu biya Naira miliyan biyu da dubu dari takwas da casa'in ( 2,890,000.00). 

A  jahar Edo za'a biya Naira miliyan biyu da dubu dari tara da sittin da takwas (2,968,000.00). sai Ekiti da Onda su kuma zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari takwas da tamanin (2,880,000.00)

Haka kuma jahohin Cross River da Osun zasu biya miliyan biyu da dubu dari tara da arba'in da takwas (2,943,000.000) da kuma miliyan biyu da dubu dari tara da casa'in da da uku (2,993,000.000)

Sai kuma jahohin Lagos da Ogun da Oyo, su kuma zasu biya naira miliyan biyu da dubu dari tara da casa'in da tara (2,999,000.000)

Sai yankunan Kudu masu Kudu da Kudu maso gabas, su kuma maniyyatan nasu zasu biya Naira miliyan biyu da dubu dari tara da sittin da takwas (2,968,000.000)

Shugaban Hukumar ta NAHCON ya ayyana kamfanonin jiragen da gwamnatin Najeriya ta sahalewa yin jigilar maniyyatan na bana da suka hada da NAHCON  Azman Air, Max Air, Air Peace, Flynas, Aero, Arik Air da kuma Value Jet Air.