Naira ta ƙara ƙarfi zuwa 1,409 kan kowace Dalar Amurka a kasuwar canji ta bayan fage, daga Naira 1,416 da aka Chanjar da ita a ranar da ta gabata.
Bayanan Babban Bankin 'Kasa CBN sun kuma nuna cewa Naira ta ƙarfafa a Kasuwar Canjin Kuɗaɗen Waje ta Najeriya, inda farashin hukuma ya inganta zuwa Naira 1,374.50 kan kowace dala daga Naira 1,378.50.
Ƙarfin da Naira ta samu ya rage tazarar da ke tsakanin farashin kasuwar bayan fage da na hukuma zuwa Naira 34.50 kan kowace dala daga Naira 37.50 da aka samu a ranar da ta gabata.
A wani bangaren kuma, yawan kuɗaɗen da aka yi cinikayya da su a kasuwar canjin kuɗaɗen waje a hukumance ya ƙaru da kashi 21.2 cikin ɗari, inda ya kai dala miliyan 322.7 daga dala miliyan 266.2 da aka samu a ranar Litinin.
Comments
Add a comment